Mayakan Haftar sun kashe yara kanana 2 a Libiya

Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libiya da Kasashen Duniya suka amince da ita a Libiya ta bayyana cewar yara kanana 2 sun mutu sakamakon harin da mayakan Haftar suka kai a kudancin Tarabulus Babban Birnin Kasar.

A rubutacciyar sanarwar da aka fitar ta shafin Faceook din hare-haren Burkhan Al-Ghadab  an bayyana cewar sakamakon makaman roka da mayakan Haftar suyka harba yankin Ayn Zara yara kanana 2 sun mutu.

Sanarwar ta kara da cewar dakarun gwamantin sun lalata wasu motocin mayakan Haftar dake kusa da garin Sirte na yankin Al-Washka.

A gefe guda shafin sada zumunta na yanar gizo mallakar mayakan Haftar ya sanar da mutuwar dakarunsu 5 a wani hari da gwamnatin Libiya ta kai da jirgin yaki mara matuki kan sansanin na 302.

A ranar 4 ga watan Afirlun 2019 ne mayakan Haftar suka fara yunkurin kwace iko da Tarabulus Babban Birnin Libiya, ita ma gwamantin kasar ta fara mayar da hare-haren martani kan dakarun 'yan tawaye.Labarai masu alaka