An kai harin bam a Mogadishu

An kai harin bam da wata mota a kusa da ginin majalisar dokokin Somaliya dake Mogadishu Babban Birnin Kasar.

An kai harin bam a Mogadishu

An kai harin bam da wata mota a kusa da ginin majalisar dokokin Somaliya dake Mogadishu Babban Birnin Kasar.

Maharan da suka nufi shingen binciken ababan hawa dake yankin Sayidka na Mogadishu ba su yi nasara ba inda ba a samu asarar rai ko dukiya ba.

Hotunan da aka fitar ta shafukan sadarwa na yanar gizo an ga yadda wuta ta kama motoci inda aka kuma aike da maa'aikatan kashe gobara.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.Labarai masu alaka