Gari guda a Mozambik ya nutse a karkashin ruwa

Garin Beira na 4 mafi girma a kasar Mozambik ya kasance a karkashin ruwa sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku.

Gari guda a Mozambik ya nutse a karkashin ruwa

Garin Beira na 4 mafi girma a kasar Mozambik ya kasance a karkashin ruwa sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku.

Sanarwar da aka fitar daga majalisar garin Beira ta ce ambaliyar ta zo a lokacinda ba a gama warkewar da ciwukan da guguwar Idai ta janyo ba.

Hotunan da majalisar ta fitar sun nuna gidaje da ababan hawa da dama dilmiye a cikin ruwa inda aka gargadi jama'a game da gurbatar yanayi bayan afkuwar ambaliyar.

Daruruwan mutane sun rasa rayukansu a 'yan kwanakin nan sakamakon ambaliyar ruwa a Gabashi da Kudancin Afirka.

Kungiyoyin kasa da kasa sun bayyana cewar dumamar yanayi ne yake janyo ibtila'İn ambaliyar ruwan.

Guguwar Idai da ta kunna kai kasashen Mozambik, Zimbabwe da Malawi a watan Maris ta rusa dubunnan gidaje da hanyoyi.Labarai masu alaka