WHO ta bukaci matan Shugabannin Afirka da su taimaka wajen yaki da cutar kanjamau

Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom ya yi kira ga matan Shugabannin Kasashen Afirka da su tashi tsaye wajen yaki da cuta mai karya garkuwar jiki musamman wajen kama jarirai a cikin iyayensu.

Adhanom ya yi jawabi a wajen taron "Afrka Mara Kanjamau" da ake gudanarwa a Kigali Babban Birnin Ruwanda kuma za a kammala a ranar 7 ga watan Disamba ya ja hankali da cewar cutar HIV, Hepatit B da Karzuwa na kara yawaita a Afirka.

Adhanom ya tunatar da cewar wadannan cututtuka na harbuwa daga iyaye mata zuwa 'ya'yan dake cikinsu, kuma ya zama wajibi a tashi tsaye wajen ganin an magance wannan matsala. Matan Shugabannin Kasashen Afirka na da babbar rawar da za su taka wajen wannan aiki.

Adhanom ya sake jan hankali da cewar nasarorin da aka samu wajen yaki da cutar kanjamau a duniya na fuskantar barazana. AKwai matsaloli na siyasa da na kudi.

Tag: WHO , Cuta , Kanjamau

Labarai masu alaka