'Yan awaren Kamaru sun kai wa jirgin saman fasinjoji hari

An bayyana cewar 'yan awaren yankin Kamaru dake magana da Turancin Ingilishi sun kai hari kan wani jirgin saman fasinjoji.

'Yan awaren Kamaru sun kai wa jirgin saman fasinjoji hari

An bayyana cewar 'yan awaren yankin Kamaru dake magana da Turancin Ingilishi sun kai hari kan wani jirgin saman fasinjoji.

Sanarwar da kamfanin jiragen sama na Kamaru Camair-Co ya fitar ta ce a lokacinda jirgin sama samfurin TJ-QDP dauke da fasijoji yake sauka a garin Bamenda na yankin da 'yan tawayen suke daga garin Doula na kasuwanci ne aka bude masa wuta.

Sanarwar ta ce sakamakon nasarar saukar da jirgin da matukinsa ya yi babu wata matsala da afku.

An sanar da cewar an dauki matakan da suka kamata a yankin kuma kamfanin ya ci gaba da jigilar fasinjoji yadda ya kamata.

Ba a bayar da wasu bayanai game da daga ina aka kai harin ko kuma su waye suka kai shi ba.Labarai masu alaka