'Yan tawaye sun kashe mutane 13 a Kongo

'Yan awaren kasar Uganda masu suna Dakarun Hadin Kan Demokradiya (ADF) sun kai hari a garin Beni na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo inda suka kashe mutane 13.

'Yan tawaye sun kashe mutane 13 a Kongo

'Yan awaren kasar Uganda masu suna Dakarun Hadin Kan Demokradiya (ADF) sun kai hari a garin Beni na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo inda suka kashe mutane 13.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa 'yan awaren sun kai hari a kauyukan Kukutama, Aveyi da Kazaroho dake da nisan kilomita 10 kudu maso-yamma da yankin Oicha.

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam da Zaman lafiya ta sanar da cewar an kai harin ne da wukake inda aka kashe fararen hula 13.

Tun bayan da dakarun Jamhuriyar Demokradiyar Kongo suka fara kai farmakai kan 'yan awaren a ranar 1 ga Nuwamba, an kashe fararen hula 123 a hare-haren ramuwar gayya da 'yan awaren ke kai wa.

 Labarai masu alaka