Cutar farankama ta yi ajalin mutane sama da dubu 5 a Kongo

Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar a tsakanin 1 ga Janairu da 17 ga Nuwamban 2019 mutane dubu 250,270 ne cutar farankama ta kama a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo inda dubu 5,110 daga cikinsu suka mutu

Cutar farankama ta yi ajalin mutane sama da dubu 5 a Kongo

Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar a tsakanin 1 ga Janairu da 17 ga Nuwamban 2019 mutane dubu 250,270 ne cutar farankama ta kama a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo. Sannan dubu 5,110 daga cikinsu sun rasa rayukansu.

Sanarwar ta ce a kokarin hana cutar ci gaba da yaduwa an yi wa yara kanana da yawa allurar riga-kafi inda aka aike da akwatuna dubu 1,137 zuwa cibiyoyin kula da lafiya a fadin kasar.

Sanarwar da UNICEF din ta fitar ta kuma ce cutar ta fi kama yara 'yan aksa da shekaru 5.

Rikicin da ake samu tsakanin 'yan aware da jami'an tsaro a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo na kawo tsaiko wajen yaki da cutar.

 Labarai masu alaka