An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 13 a Najeriya

A wasu farmakai da aka kai a yankin arewa maso-gabashin Najeriya dake Yammacin Afirka an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 13.

An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 13 a Najeriya

A wasu farmakai da aka kai a yankin arewa maso-gabashin Najeriya dake Yammacin Afirka an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 13.

Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Aminu Iliyasu ya shaida cewar an kai hari kan 'yan ta'addar na Boko Haram a yankin Duguri dake jihar Borno.

Ilyasu ya kara da cewa a yayin farmakin an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 13 inda wasu da dama da aka jikkata suka gudu.

Iliyasu ya ce an jikkata sojoji 4 a harin kuma an kwace makamai da kayan fadar 'yan ta'addar.

Kwanaki 2 da suka gabata ma dakarun Najeriya sun kashe 'yan ta'addar 9 a wani farmaki da suka kai musu.Labarai masu alaka