An kashe sojojin Burundi 10 a harin kwantan bauna daka kai musu

Sojojin Burundi 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin kwantan bauna da aka kai musu a iyakar kasar da Ruwanda.

An kashe sojojin Burundi 10 a harin kwantan bauna daka kai musu

Sojojin Burundi 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin kwantan bauna da aka kai musu a iyakar kasar da Ruwanda.

Majiyoyin sojin kasar sun bayyana cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai harin kwantan bauna kan cibiyar soji dake kauyen Mabayi mai nisan kilomita 100 daga tsohon Babban Birnin Kasar Bujumbura.

Majiyar ta bayyana cewar akalla sojoji 10 ne suka mutu kuma wasu 10 sun bata. An kuma kubutar da wasu sojojin 15 daga harin.

Mahukuntan ba su bayyana ko su waye maharan ba wadanda suka saka sulke da kuma rufe fuskokinsu a lokacinda suka kai harin.

Wannan hari ne mafi muni da aka kai wa sojoji a Burundi tun shekarar 2015.

Tag: Burundi , Hari

Labarai masu alaka