An kama wasu manyan kwamandojin Boko Haram 8 a Legas

A Najeriya an kama wasu manyan kwamandojin kungiyar ta'adda ta Boko Haram su 8.

An kama wasu manyan kwamandojin Boko Haram 8 a Legas

A Najeriya an kama wasu manyan kwamandojin kungiyar ta'adda ta Boko Haram su 8.

Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya ta 81 dake Legas Manjo Janar Olu Irefin ya ce a karkashin hare-haren "Murmushin Kada" da ake kai wa a arewa maso-gabashin Najeriya an kama wasu wamnayn kwamandojojin Boko Haram 8 a Legas.

Janar Irefin ya kara da cewar an kuma kwace wasu manyan makamai daga hannun 'yan ta'addar.

A farmakan da aka kai a yankin Gida Dubu, Fadaman Mada, Turum da Bakaro dake jihar Bauchi kuma an kama mambobin kungiyar ta Boko Haram 72 tare da kwace makamai daga hannunsu.

Haka zalika an kwace layukan wayoyin hannun 'yan ta'addar.Labarai masu alaka