Rigima a Jami'ar Kogi ta kashe mutane 13

Mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata rigima da ta barke a Jami'ar Kogi dake Najeriya.

Rigima a Jami'ar Kogi ta kashe mutane 13

Mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata rigima da ta barke a Jami'ar Kogi dake Najeriya. 

Kafafen yada labaran kasar sun tabbatar da cewa mutane 13 ne suka rasu sakamakon wata rigima da ta barke tsakanin daliban jami'a inda aka kai mutane da dama asibiti.

Mai magana da yawun Rundunar 'Yan Sandan Jahar Kogi Hakeem Busari ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro jami'ar inda aka fara gudanar da bincike mai zurfi game da al'marin. 

Ila yanzu dai babu wani cikekken bayani game da sababin rikicin. 

Gwamnan Jahar Yahaya Bello ya ce yana taya iyalen wadanda suka rasu kuka yayinda ya ce za a gudanar da bincike mai zurfi game da al'amarin sannan a hukunta masu lefi. 

Labarai masu alaka