An kashe Fulani 15 a wani hari a Najeriya

Fulani 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu a tsakiyar Najeriya.

An kashe Fulani 15 a wani hari a Najeriya

Fulani 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu a tsakiyar Najeriya.

Sanarwar da Sakatare Janar na Kungiyar Miyetti Allah Muhammad Mainasara ya fitar ta bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun kai wa Fulani hari a jihar Kogi.

Mainasara ya ce, an kashe Fulani 15 a harin tare da hallaka shanu da dama.

A gefe guda kuma gwamnan Kogi Yahya Bell ya fitar da sanarwa game da harin inda ya ce, idan jama'ar yankin ba su fito da maharan ba a cikin kwanaki 7 to za a sauke su daga mukamansu.

Bello ya kara da cewar an aike da karin jami'an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru.

Ya ce "ba zan iya yin siyasa ta hanyar wasa da rayukan mutane ba. Saboda haka ina gargadin masu haifar da sabon rikici saboda siyasa."Labarai masu alaka