Dakarun Libiya sun kai wa mayakan Haftar hari

Dakarun gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya sun kai hare-hare ta sama kan mayaka masu goyon bayan Janar Haftar Khalifa a garin Geryan dake gabashin kasar.

Dakarun Libiya sun kai wa mayakan Haftar hari

Dakarun gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya sun kai hare-hare ta sama kan mayaka masu goyon bayan Janar Haftar Khalifa a garin Geryan dake gabashin kasar.

Kakakin dakarun gwamnatin hadin kan kasar Muhammad kanunu ya fitar da wata rubutacciyar sanarwa cewa, jiragen samansu na yaki sun kai hare-hare a wurare 6 da dakarun haftar suke.

Sanarwar ta ce, hare-haren sun nufi inda ake sauke makamai da kayan yaki na magoya bayan Haftar.

A gefe guda an sanar da samun kazafin fada tsakanin bangarorin biyu a kudancin Tarabulus inda babu wani bangare da ya samu wani cigaba.

Haftar ya shiga garuruwa da dama ba tare da fada ba da suka hada da Sabrata, Surman da Geryan. Kuma bayan farfagangar kudi da tattalin arziki da suka yi kungiyoyi da dama da suke dauke da makamai sun mara wa Haftar baya.

 Labarai masu alaka