Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 37 a Afirka ta Kudu

Ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa sun afku a jihar KwaZulu-Natal dake Afirka ta Kudu inda suka janyo asarar akalla rayuka 37.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 37 a Afirka ta Kudu

Ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa sun afku a jihar KwaZulu-Natal dake Afirka ta Kudu inda suka janyo asarar akalla rayuka 37.

Ministan jihar KwaZulu-Natal Nomusa Dube-Ncub ya ce, an samu ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a yankin dake gabar teku na jihar.

Ya ce, mutane 37 sun mutu inda wasu da suka raunata sakamakon Ibtila'in kuma an nemi wasu da dama an rasa.

A gefe guda Dakarun Tsaron Afirka ta Kudu (SANDF) sun aike da jami'an ceto zuwa yankin.

Mahukunta na fargabar adadinw adanda za su mutu na iya daduwa.Labarai masu alaka