An kashe mutane 17 a wani hari da aka kai a jihar Benue ta Najeriya

Mutane 17 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu masu dauke da makamai suka kai a Najeriya.

An kashe mutane 17 a wani hari da aka kai a jihar Benue ta Najeriya

Mutane 17 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu masu dauke da makamai suka kai a Najeriya.

Kakakin 'yan sandan jihar Benue Iterver Akase ya fadi cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai farmaki a yankin Agatu inda suka kashe kashe mutane 17 tare da jikkata wasu da dama.

Akase ya ce, an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti inda aka kuma fara gudanar da bincike.

Ana yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

Makiyaya Fulani dake tafiya zuwa kudancin Najeriya inda manoma ke yawan satar shanunsu wanda hakan ke janyo rikici da sarar rayuka da dukiyoyi.

Labarai masu alaka