An saki wasu 'yan kasar Tunisiya da aka yi garkuwa da su a Libiya

A garin Zawiya na kasar Libiya an saki 'yan kasar Tunisiya 14 da wasu masu dauke da makamai suka yi garkuwa da su.

An saki wasu 'yan kasar Tunisiya da aka yi garkuwa da su a Libiya

A garin Zawiya na kasar Libiya an saki 'yan kasar Tunisiya 14 da wasu masu dauke da makamai suka yi garkuwa da su.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Tunisiya ta ce, aranar Alhamis din makon da ya gabata ne a garin Zawiya na Libiya aka yi garkuwa da Tunisiyawan su 14 dake aikin kwadago.

An bayyana cewar, leburorin da suke a hannun 'yan sandan Zawiya na cikin kyakkawan yanayi.

Sanarwar ta kuma ce, an samu nasarar sallamar mutanen da Ministan Harkokin Wajen Tunisiya Hamis Al-Jihinawi ya tattauna da takwaransa na Libiya Muhammad Tahir, kuma gwamnatin Tunus ta mika godiya ga ta Tarabulus.

Jaridun Tunisiya sun ce, a garin na Zawiya an yi garkuwa da 'yan kasarsu 14 da suka hada da masu aiki a matatar man fetur 12. 

An bayyana cewar kungiyar masu dauke da makamai ta dauki wannan mataki ne don mayar da martanin daure wani dan Libiya a kurkukun Tunisiya.Labarai masu alaka