An bayar da dama a ci gaba da yakin neman zabe a Najeriya

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta Najeriya ta sake bayar da izinin a ci gaba da yakin neman zabe a kasar bayan dage lokacinsa da ta yi.

An bayar da dama a ci gaba da yakin neman zabe a Najeriya

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta Najeriya ta sake bayar da izinin a ci gaba da yakin neman zabe a kasar bayan dage lokacinsa da ta yi.

Rubutacciyar sanarwar da hukumar ta fitar ta ce, sakamakon gana wa da jam'iyyun siyasar kasar an ba wa 'yan takara ci gaba da yakin neman zabe har na da ranar Alhamis 21 ga watan Fabrairu.

A ranar 16 ga Fabrairu Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta shirya gudanar da zaben Shugaban Kasa amma saboda matsalar kayan aiki ta dage shi zuwa 23 ga watan.

Tag: Zabe , Najeriya

Labarai masu alaka