Ebola ta yi kaka gida a Kongo

Jama'a a Demokradiyyar Kongo na ci gaba da rasa rayukan sakamakon annobar Ebola da ta yi kaka gida a kasar.

Ebola ta yi kaka gida a Kongo

Jama'a a Demokradiyyar Kongo na ci gaba da rasa rayukan sakamakon annobar Ebola da ta yi kaka gida a kasar.

Cutar wacce ta bulla tun a watan Yulin da ya gabata,ta yi sanadiyyar rayukan 220 ya zuwa yanzu,inda a jiya 4 ga watan Disamban shekarar 2018 kawai, ta  rutsa da wasu karin rayuka 8.

A cewar alkalumman ma'aikatar kiwon lafiyar Demokradiyyar Kongo dangane Ebola wacce ta fara kuno kai a yankin Beni gabanin ta ci gaba da yaduwa zuwa Ituri,ya zuwa yanzu akwai akalla mutane da 453 wadanda ake kyautata zaton sun kamu da cutar,inda 405 daga cikin su aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayoyin Ebola.

Tun barkewar cutar kawo yau, mutane 220 ne suka rasa rayukansu dalilin wannan annabor, wasu 144 kuma,sun tsalake rijiya da baya ta hanyar warkewa daga cutar.Bugu da kari,akwai mutane 48 daga cikin 453 daga ke aman jini,wadanda suka mutu ba tare da an tantanci ko Ebola ce ta kashe su ko kuma a'a.

Shugabannin  Demokradiyyar Kongo sun dauki matakan yi wa al'umar yankunan da lamarin ya shafa,allurar riga-kafi tun a ranar 8 ga watan Yulin da ya gabata,inda a yanzu kusan mutane dubu 39 da 845 suka ci ribar wannan shirin.

A gefe daya kuma, kuma ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar, ta kaddamar da wata gasar kwallon kafa mai taken "Ebola ba ta a muhallina" da zummar kara karfafa gwiwar al'uma wajen yakar annobar da ke ci gaba barna a Kongo.

A tsawon mako daya, kungiyoyin wasa 47 zasu yi gogayya da juna a wannan gasar wacce aka shirya ta a yankunan da Ebola ta durkusarwa,ganin yadda kwallon kafa ke da farin jini tsakanin matasan kasar.

Ministan kiwon lafiya na kasar Demokradiyyar Kongo,Oly Ilunga ne ya fara buga kwallon farko a wannan gasar ta nufin share fage.

Cutar Ebola ta bulla a kasar Demokradiyyar Kongo a karo na farko a shekarar 1976,inda a watan Disamban 2013 ta kutsa kai zuwa kasashen yammacin Afirka.A shekarar 2014 zuwa 2017 ta isa kasashen Ginea,Liberia da kuma Saliyo,inda ta kama akalla mutane dubu 30,wadanda dubu 11 daga cikin su suka rasa rayukansu.


Tag: kongo

Labarai masu alaka