An tuhumi firaministan Mali da kisa

An zargi firaministan Mali,Soumeylou Boubèye Maïga da samun hannu dumu-dumu a kisan wasu 'yan jaridan kasar Faransa biyu.

An tuhumi firaministan Mali da kisa

An zargi firaministan Mali,Soumeylou Boubèye Maiga da samun hannu dumu-dumu a kisan wasu 'yan jaridan kasar Faransa biyu.

Maiga,wanda ya rika mukamin ministan tsaro kasa a lokacin da wannan lamarin ya afku (2013), ya yi watsi da wannan zargin,inda ya ce kage ne aka yi masa.

A ranar Asabar din nan, kafafan yada labaran kasar Faransa sun bankado wasu sabbin hujjojin da ke nuna cewa firaministan na a sahun wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen salwanta rayukan yan Jarida,Ghislaine Dupont da Claude Verlon.

Wannan shi ne karo na farko da aka ambaci sunan wani babban jiga-jigin gwamnatin Bamako tun a lokacin da aka fara bincike kan wannan lamarin ,inji rediyon kasar Faransa RFI.

Wani mashaidi ya sanar da cewa,wanda ya yi garkuwa da Dupont da Verlon tare da halaka su,wato Baye Ag-Bakabo na da alakar kud-da-kud da minista Maiga.

An kashe dan jarida Ghislaine Dupont da takwaransa mashiryi Claude Veron a ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar 2013 a jihar Kidal da ke arewa maso gabashin Mali,inda suka kai ziyara da zummar hada wani shirin talabijin mai suna "Rikicin Arewacin Mali da hanyar Samar da Sulhu".

Kwanaki hudu da mutuwar 'yan jaridan,wasu mutane wadanda suka sanar da cewa, mambobi ne su na kungiyar ta'adda ta AQMI,sun fito fili don daukar alhakin aikata wannan ta'asar.

Tun a wannan lokacin kawo yanzu,Mali da Faransa ke ci gaba da zurfafa bincike don gane ainahin musababbin wannan ta'adi.


Tag: kisa , jarida , faransa , mali

Labarai masu alaka