An sassauta dokar hana fita a jihar Kaduna dake Najeriya

Gwamnatin jihar Kaduna ta bakin kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ta sanar da sassauta dokar hana fita ta awanni 24 da aka saka sakamakon rikicin kabilanci da addini da ya barke a karshen makon da ya gabata.

1075206

A sanarwar da kakakin gwaman na Kaduna Aruwan ya fitar ya ce, daga yanzu jama'a za su iya fita waje daga karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma.

A makon da ya gabata ne aka fara wani rikicin kabilanci a yankin Kasuwan Magani da ke Kudancin jihar ta Kaduna inda sama da mutane 55 suka mutu.

Jihar Kaduna dai ta dade tana fama da rikice-rikicen kabilanci da na manoma da makiyaya.

Labarai masu alaka