Mutane 35 sun mutu sakamakon kama wuta da tankar mai ta yi a Najeriya

Mutane 35 ne suka mutu yayinda wasu daruruwa suka jikkata sakamakon kama wa da wuta da motar tanka dauke da man fetur ta yi a jihar Nassarawa da ke tsakiyar kasar.

Lamarin ya afku a wani gidan sayar da mai da ke hanyar Lafia-Makurdi da ta hada kudanci da arewacin Abuja.

Jami'in Hukumar Bayar da Agaji ta Kasa Usman Ahmad ya ce, fashewar ta afku a lokacinda tankar ke sauke mai a gidan man.

Rahotannin farko sun ce, mutane 35 ne suka mutu yayinda wasu daruruwa suka jikkata.

Dalilin yawaitar mamatan da wadanda suka jikkata shi ne yawaitar mutane a lokacinda lamarin ya afku.

Usman Ahmad ya kuma ce, mafi yawan wadanda suka mutu mutanen da suka je kallo ne bayan fashewar ta afku.

A watan Yuni ma wata tankar mai ta kama da wuta a jihar Legas da ke Najeriya inda mutane 9 suka mutu motoci sama da 52 suka kone kurmus.Labarai masu alaka