Wasu makiyaya sun kashe ‘yan sanda uku a Taraba

Akalan ‘yan sanda uku wasu makiyaya suka kashe bayan sun yi musu kwanton bauna a kauyen Bujum Kasuwa dake jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu makiyaya sun kashe ‘yan sanda uku a Taraba

Akalan ‘yan sanda uku wasu makiyaya suka kashe bayan sun yi musu kwanton bauna a kauyen Bujum Kasuwa dake jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba David Misal ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu da cewa an yiwa jami’an tsaronmu kwantaon bauna a yayinda suke wata rangadi a karamar hukumar Lau.

Misal ya kara da cewa baya ga ‘yan sanda uku an kuma kashe ‘yan banga biyu. Taraba dai na daya daga cikin jahohin da ake samun rashin jituwan manoma da makiyaya.

Dukkanin bangarorin biyu na zargin jami’an tsaro da yin rashin adalci.

AALabarai masu alaka