‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Najeriya

Akalla mutane 11 ne suka mutu yayinda wasu 12 suka jikkata sakamakon harin da ‘yan bindinga suka kai a jihar Plateau da ke Tsakiyar Najeriya.

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Najeriya

Akalla mutane 11 ne suka mutu yayinda wasu 12 suka jikkata sakamakon harin da ‘yan bindinga suka kai a jihar Plateau da ke Tsakiyar Najeriya.

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun bude wuta kan jama’ar kauyen Lo Pamyeti da ke jihar ta Plateau.

‘Yan sandan jihar sun bayyana cewa, a daren ranar da aka kai harin an yi musu waya tare da sanar da su cewar garin na fuskantar hari, kuma nan da nan suka tura dakaru inda suka je suka tarar da gawarwarkin mutanen da aka kashe.

N kai mutanen Babban Asibitin Koyarwa na Jos inda 11 daga ciki aka tabbatar sun mutu, wasu 12 da suka jikkata kuma suke ci gaba da karbar magani a asibiti.

Jihar Plateau dai na fama da rikicin kabilanci da na manoma da makiyaya.

Ba a kama kowa ba game da harin amma an fara gudanar da bincike.Labarai masu alaka