'Yan adawa a Sudan ta Kudu sun amince da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

'Yan adawar Sudan ta kudu sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayanda Shugaban kasar Sudan Umar Al-Bashir ya ba su garantin Kungiyar Cigaban Kasashe ta IGAD za ta tattauna kan kasarsu a babban taronta na watan Satumba.

Shugaban Kungiyar 'yan adawa mafi girma kuma mai dauke da makamai da ke kasar Riek Machar tare da wasu kungiyoyi 9 sun hadu tare da kafa Kungiyar 'Yan Adawa ta Sudan ta Kudu (SSOA) inda a sanarwar da suka fitar sun bayyana cewar bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Khartoum sun mika wa Shugaba Al-Bashir rubutacciyar takarda kan abubuwan da suke bukata.

A sanarwar tasu sun bukaci a sauya tsarin daukar matakai da hukunci, ba za a yi wani sauyi ga yarjejeniyar ba ba tare da sanin bangarorin ba, a kawo takardar tabbatar da kafa jihohi a hada ta da yarjejeniyar, Kundin tsarin mulki ya zama wanda zai kunshi abubuwan da jama'a suke so, sannan a saka kasashen Sudan, Uganda, Kenya da Itopiya a jerin kasashen da za su zama garanto kan yarjejeniyar.

A ranar Alhamis din nan ne Machar da sauran kungiyoyi 9 suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar a Sudan.

A shekarar 2011 ne Sudan ta Kudu ta balle daga Sudan inda a shekarar 2013 kuma ta fada yakin basasa bayan da Shugaban kasar Salva Kiir ya zargi mataimakinsa Riek Machar da yunkurin yi masa juyin mulki.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da IGAD ta jagoranta amma an sake samun barkewar rikici a 2016.Labarai masu alaka