Mutane 17 sun mtu a hatsarin jirgin sama a Itopiya

Mutane 17 ne suka mutu sakamakon hatsarin jirgin saman sojin Itopiya wanda ya fado a kan hanyarsa ta zuwa Bushoftu daga Dire Dawa.

Mutane 17 sun mtu a hatsarin jirgin sama a Itopiya

Mutane 17 ne suka mutu sakamakon hatsarin jirgin saman sojin Itopiya wanda ya fado a kan hanyarsa ta zuwa Bushoftu daga Dire Dawa.

Dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin da suka hada da sojoji sun mutu a hatsarin jirgin samfurin ET-AIU wanda ya fado a yankin Shoa da ke da nisan kasa da kilomita 100 daga Addis Ababa Babban Birnin Kasar.

An fara gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin.

Kamfanin dillancin labarai na Itopiya ENA ya sanar da cewar jirgin ya fara kama wa da wuta a sama kafin ya fado.

 Labarai masu alaka