Zaftarewar kasa ta kashe yara kanana 5 a Bangaladash

Yara kanana 5 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa ta janyo a kusa da sansanin da gwamnatin Bangaladash ta ajje 'yan gudun hijirar Musulman Arakan 'yan kasar Myammar.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito 'yan sanda na cewa a yankin Cox Bazar an samu ruwan sama na tsawon kwanaki 3 inda ya ra a 5 suka mutu a kusa da sansanin da Musulman Arakan suke.

An bayyana cewa, wadanda suka mutu din ba Musulman Arakn ba ne kuma masu aiyukan ceto sun yi gargadin yiwuwar samun babban ibtila'i a yankunan da ruwan saman ya yi karfi.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun ce, daga 25 ga watan Agustan 2017 zuwa yau Musulman Arakan sama da dubu 700 ne suka gudu tare da neman mafaka a Bangaladash.

Tag: Siyasa , Afirka

Labarai masu alaka