Turkiyya ta yi farin cikin yarjejeniyar lumanar Ethiopia da Eritrea

Turkiyya ta bayyana farin cikinta akan yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Ethiopia ta yi da ƙasar Eritrea.

Turkiyya ta yi farin cikin yarjejeniyar lumanar Ethiopia da Eritrea

 Turkiyya ta bayyana farin cikinta akan yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Ethiopia ta yi da ƙasar Eritrea.

Ma'aikatan harkokin wajen Turkiyya ta fitar da sanarwar cewa:

Turkiyya na matukar farin cikin yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Ethiopia ta yi da Eritrea domin samar da lumana a tsakanin su da kuma daidaito da zaman lafiya a Afrika. Rataba hannu akan warware matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu da shugaban kasar Ethiopia Abiy Ahmed ya yi da takwaransa na Eritrea a birnin Asmara abin farin ciki ne sosai.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan yarjejeniyar zaman lafiyar zai bunƙasa kasashen biyu dake makwabtaka da juna da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Ministan yaɗa labaran kasar Eritrea Yemane Gebremeskel ya fitar da wata sanarwa ta shafukansa na sada zumunta da cewa shugaban ƙasar Ethiopia Abiy Ahmed da takwaransa na Eritrea lsaias Afewerki sun rataɓa hannu a birnin Asmara domin samar da lumana tsakanin ƙasashen biyu.Labarai masu alaka