Cutar Kwalara na ci gaba da kama mutane a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Annobar cutar kwalara na ci gaba da kama jama'a a Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Cutar Kwalara na ci gaba da kama mutane a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Annobar cutar kwalara na ci gaba da kama jama'a a Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Gwamnan jihar Alphonse Ngoyi Kasanjiya zanta da manema labarai inda ya ce, a garin Mbujimayi an sanar da sake ganin bullar cutar ta Kwalara ko amai da gudawa.

Kasanji ya ce, alkaluman da ke hannunsu sun nuna yadda a cikin watanni 4 mutane 833 suka kamu da cutar kuma 104 daga cikinsu sun mutu.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, cutar ta sake bulla a wasu unguwanni saboda yadda jama'a suke shan ruwan sha mara tsafta inda ya yi kira ga gwamnatin kasa da ta kai wa yankunan taimakon gaggawa.

Alkaluman da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta fitar a ranar 14 ga watan Yuni sun bayyana cewa, daga farkon shekara zuwa yau mutane dubu 1,699 ne suka kamu da cutar Kwalara inda 333 suka mutu a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Jihar Kasai na da mutane miliyan 2 kuma yankin Mbujimayi mafi yawna jama'a ne ya fi kamu wa da cutar ta amai da gudawa.Labarai masu alaka