An bukaci a a yi afuwa ga sojojin Najeriya da suke daure

Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai da ke Najeriya Albarkacin Watan Ramadhan ta nemi da a yi afuwa ga wasu jami'an sojin Najeriya da suke daure da kuma wadanda ake ci gaba da yi wa Shari'a saboda kin yakar 'yannta'addar Boko Haram.

A karshen shekarar 2014 an yanke hukuncin daurin rai da rai a gidan yari ko na kisa ga sojoji 66 saboda bore da suka yi wa manyansu tare da kin yakar 'yan ta'addar Boko Haram.

Lamarin ya afku a zamanin Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan amma gwamnatin Muhammadu Buhari ta rage hukuncin zuwa shekaru 10.

Kungiyar ta ce, ci gaba da tsare sojojin a gidan yari ba daidai ba ne saboda an kama su ne sakamakon tona asirin sace dala biliyan 2.1 da gwamnati ta ware don yaki da Boko Haram. 

Akwai jami'an sojin Najeriya da dama da ke daure wanda kungiyar ke neman a yi musu afuwa a sake su albarkacin wannan wata na Ramadhan da aka kammala azumta.

Tag: MURIC , Sojoji , Afuwa

Labarai masu alaka