Sojoji 2 sun mutu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Aljeriya

Sojoji 2 ne suka mutu inda wani 1 ya jikkata sakamakon fadowar wani jirgin sama mai saukar ungulu a yamma da Algiers babban birnin kasar.

Lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin yake sintiri a yankin Naam.

Kafar talabijin ta Al-Nar ta bayar da labarin cewa, hukumomin kasar ba su ce komai game da lamarin ba.

Amma kafar talabijin ta Echorouk ta tabbatar da cewa, jirgin mallakar sojojin da ke kula da kan iyakokin Algeriya ne.

Jami’an tsaro na farin kaya sun taimaka wajen kashe wutar da ta kama jirgin tare da kubutar da soja 1 da ya samu raunuka.

Wannan ne karo na 2 a cikin wata 1 da abu irin wannan ya faru a Aljeriya inda a ranar 21 ga watan Mayu ma’aikatar tsaro ta sanar da mutuwar sojojinta 3 sakamakon hatsari a jirgi mai saukar ungulu.Labarai masu alaka