Ebola na kisa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Adadin wadanda suka muta sakamakon kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya kai mutane 42.

Ebola na kisa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Hukumar kula da Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a kasarJamhuriyar Demokradiyar Congo ya kai mutane 42 daga cikin mutane 70 da suka kamu da cutar.

Wannan adadi ya hada ma'aikatan lafiya takwas da suka kamu da Ebola, a kasar da aka fara gano cutar a shekarar 1976.

Ga dukkan alamu kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na shiga tsaka mai wuya, inda bayan wani bin diddigi akan mutane 939, aka samu 628 daga cikinsu na dauke da cutar.

Hukumar ta WHO ta sanar da cewa, “a cikin mutane 311 da aka duba lafiyarsu a ranar 24 ga watan Satumba, 290 (93%) daga cikinsu na dauke da cutar Ebola”.

Haka zalika an bayyana cewa, yanayin bullar cutar da ta kashe mutane a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ba shi da alaqa da wanda ya kashe mutane fiye da 3000 a kashen Guinea, Liberia da Sierra Leone da Najeriya dake yammacin Afirka.


Tag:

Labarai masu alaka