Wata sabuwar cuta na kisa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Wata sabuwar cuta da ba a san irin ta ba na daukar rayukan mutane a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, kuma Hukumar kula da Lafiya ta Duniya ta ce cutar ba Ebola ba ce.

Wata sabuwar cuta na kisa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta bayyana cewar mutane 13 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ya zuwa yanzu.

Alamun cutar da take da tasiri a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun yi kama da na cutar Ebola da ta addabi yammacin Afirka, wato zazzabi, amai da gudawa.

Hukumomin kasar sun ce sakamakon cewa da ake cutar Ebola ce, an dibi jinin mutane don aunawa a gano ko wacce irin cuta ce.

Ministan lafiya na kasar ya bayyana cewar mutane 13 ne suka mutu inda biyar daga cikinsu ma'aikatan lafiya ne sai kuma masu dangantaka da marasa lafiyar ko wadanda suka sanya hannu wajen shirya gawarwaki.

Ministan ya kuma kara da cewar akwai mutane 80 da aka tsare da ake zargin sun ka u da cutar inda za a binciki lafiyarsu.

Ana dai fargaba sosai game da cutar sakamakon mutuwar sama da mutane 1,400 a kasashen Liberia, Sierra Leone, Guinea da Najeriya bisa kamuwa da cutar Ebola.

A shekarar 1976 ne aka fara ganin cutar Ebola a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo inda har aka ayyana dokar ta baci.


Tag:

Labarai masu alaka