An sake yanke hukuncin kisa a Masar

A birnin Iskandariyya an yankewa wani mutum dake adawa da gwamnatin da ta yi juyin mulki a kasar hukuncin kisa, inda aka yankewa wasu mutane 18 hukuncin daurin rai da rai.

An sake yanke hukuncin kisa a Masar

A kotun birnin Iskandariyya dai ana tuhumar wasu mutane 63 da ake zargi da kashe wani matashi mai goyon bayan gwamnatin sojin kasar.

Kotun dai ta tuhumi mutanen dake zanga-zangar nuna adawa da kifar da zababbiyar gwamnatin Muhammad Mursi wanda soji suka yi, inda mutanen suka jefo wani

matashi mai goyon bayan sojin daga kan wani dogon gini kuma ya rasa ransa a sakamakon hakan, a saboda haka kotun ta yankewa mutum 1 hukuncin kisa, 18

daurin rai da rai.

An kuma bayyana cewa sauran mutanen da aka tuhuma kuma kotun ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari daga shekaru 7 zuwa 15.

A yankin Sidi Jabir dake birnin Iskandariyya, a ranar 5 ga watan Yunin shekara ta 2013, sakamakon arangama tsakanin masu adawa da masu goyon bayan juyin

mulkin kasar ta Masar, aka tuhumi mutane 63 kamar yadda aka tuhumi mambobin kungiyar 'yanuwa musulmi da laifin kisan kai da mallakar makamai.

A gefe guda kuma. A birnin Alkahira kuma an ba da hutun zaman shari'ar hambararren shugaban kasar ta Masar Muhammad Mursi tare da wasu mutane 130 har

sai nan da 7 ga watan Yuni.


Tag:

Labarai masu alaka