Kungiyoyi na ci gaba da nuna wa duniya motocin da za su shiga gasar Formula 1 da su a bana

Kungiyoyin da za su halarci gasar tseren motoci ta Formula 1 da za a fara nan da wasu 'yan kwanaki na ci gaba da nu8na wa duniya motocin da za su fafata da su a gasar.

Kungiyoyi na ci gaba da nuna wa duniya motocin da za su shiga gasar Formula 1 da su a bana

Kungiyoyin da za su halarci gasar tseren motoci ta Formula 1 da za a fara nan da wasu 'yan kwanaki na ci gaba da nuna wa duniya motocin da za su fafata da su a gasar.

Bayan kungiyoyin Haas, Toro Rosso da Williams, Mercedes da Renault ma sun baje-kolin nasu motocin.

Mercedes da tun shekarar 2014 suka hana kowa zama a kan gaba a gasar sun bayyana mota samfurin W10.

Motar ta bana ta dan bambanta da wadda kungiyar ta yi amfani da ita a shekarar 2018 da ta gabata wadda kan wannan yake da wata kalar azurfa da tauraro.

Kungiyar Renault kuma ta bayyana tata motar da za ta yi amfani da ita a 2019.

Motar ita ce RS19 wadda kıke da launukan baki da ruwan dorawa.Labarai masu alaka