Premier League: Liverpool ta sake hawa tebur

A gasar English Premier League da aka kara tsakanin Liverpool da Bournemouth, Ƙungiyar Liverpool ta sake hawa kan tebur bayan ta doke Bournemouth da ci 3-0

Premier League: Liverpool ta sake hawa tebur

A gasar English Premier League da aka kara tsakanin Liverpool da Bournemouth, Ƙungiyar Liverpool ta sake hawa kan tebur bayan ta doke Bournemouth da ci 3-0

A yayinda ake mako na 26 Liverpool ta jefa kwallaye uku a ragar Bournemouth a mintuna na 24 wanda Sadio Mane ya jefa sai kuma a minti na 34 ta Georginio Wijnaldum da kuma na minti 48 wanda dan kasar Misira Muhammed Salah ya jefa.

Liverpool ta hau teburin da maki 65 inda Manchester City ke binta baya da maki 62. Ƙungiyar Bournemouth ta kasance mai maki 33 inda ta kasance ta 11 a teburin.

Arsenal wacce ke kokarin zuwa na huɗu ta ja daga da Huddersfield Town inda aka tashi 2-1

A wasan da Mesut Özil bai kasance cikin yan wasa 18, Alex lwobi ya jefa kwallo raga a minti na 16; a yayinda Alexander Lacazette ya ƙara daya a minti na 44. Ita kuwa Hunderfield Town ta jefa kwallo daya tilo ne ta ɗan wasa Sead Kolasinac a minti na 90+3.

Arsenal wacce ta kasance ta 6 da maki 50 ta bar Hunderfield Town ta baya da maki 11.

 Labarai masu alaka