Gawar da aka tsinta ta Emiliano Sala ce

An gano cewa gawar da aka tsinta a gabar mashigin English Channel na kasar Burtaniya ta sanannen dan wasan kwallon kafar kasar Argentina,Emiliano Sala.

Gawar da aka tsinta ta Emiliano Sala ce

An gano cewa gawar da aka tsinta a gabar mashigin English Channel na kasar Burtaniya ta sanannen dan wasan kwallon kafar kasar Argentina,Emiliano Sala.

A cewar wata sanarwar da 'yan sandan yankin Dorset na kudu maso yammacin Ingila suka fitar,an dai tsamu gawar  daga teku a tsakiyar sassan wani jirgin sama wanda ya fado makwanni uku da 'yan kai da suka gabata.

A sanarwar an kara da cewa,tuni aka bai wa iyalin marigayin dan wasan da na matukin jirgin sama,David Ibbotson labarin afkuwar wannan mummunan lamarin.
An dai tanadi wasu kwararrun jami'ai na musamman wajen kwantar wa makusantan mamatan hankali da kuma ba su duk wani tallafi da suke bukata.

A ranar 22 ga watan Janairun bara,wani karamin jirgin saman da ke dauke da Sala da Ibbotson ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Nantes na kasar Faransa da zummar zuwa birnin Cardiff,helkwatar karamar hukumar Galler da ke Ingila, yayi layar zana a sararin samaniyar Mashigin English Channel.Abinda yasa Tuni aka fidda rai da ganin su salim-alim.

A ranar 3 ga watan Fabrairun bana an gano sassan jirginsu a wani yankin na Mashigin English Channel,wanda haka yasa aka daura damarar gudanar muhimman aiyukan gano gawarwakin da ke cikin shi.

A ranar 6, an aika gawar da aka gano zuwa tsibirin Portland don samun cikakken bayani a kanta,yayin da ake kyautata zaton cewa mummunan yanayi da matsalolin da suka jibanci inji ne ummal'aba'isar afkuwar wannan hatsarin.

An sanar da cewa,dan wasa Sala ya rattaba hannu a wata yarjejeniyar da ta haura Fam milyan 15 wacce za ta ba shi damar ci gaba da taka leda a Kungiyar Cardiff City ta Premier League.Labarai masu alaka