Real Madrid na son sayen Hazard kan Fan miliyan 100

Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid dake Spaniya ta bayyana sha'awar sayen dan wasan kasar Beljiyom dake taka leda a kungiyar Chelsea dake Ingila Eden Hazard kan kudi har Fan miliyan 100.

Labaran da jaridar Telegraph ta fitar na cewa, real Madrid ta bayyana sha'awar sayen Hazard kan Fan Stalin miliyan 100.

Kungiyar ta Ingila ma ta tabbatar da real Madrid ta nemi sayen Hazard din.

A tattawaunawar da Hazard ya yi a gidan rediyon Faransa ya ce, bai san abinda zai yi ba, ya riga ya yanke hukuncinsa.

Hazard aya fadi cewar a baya ya so ya taka leda a Real Madrid kuma ga dukkan alamu a karshen kakasar wasanni ta bana zai koma kungiyar.Labarai masu alaka