Manchester Citiy ta doke Everton da ci 2 da nema

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester ta doke takwararta ta Everton da ci 2 da nema a gasar Premier League ta kasar Ingila.

2019-02-06T213311Z_1285180594_RC1ED4D59A00_RTRMADP_3_SOCCER-ENGLAND-EVE-MCI.JPG
2019-02-06T212630Z_2130503403_RC1C40EB8940_RTRMADP_3_SOCCER-ENGLAND-EVE-MCI.JPG
2019-02-06T214515Z_757004450_RC151C508350_RTRMADP_3_SOCCER-ENGLAND-EVE-MCI.JPG
2019-02-06T214618Z_967020417_RC125FDAAE60_RTRMADP_3_SOCCER-ENGLAND-EVE-MCI.JPG

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta doke takwararta ta Everton da ci 2 da nema a gasar Premier League ta kasar Ingila.

A wasan da aka buga a mako na 26 na gasar a filin wasanni na Goodison Park Manchester City ta samu nasara a kan Everton da ci 2 da nema.

Kwallayen da daliban Pep Guardiola suka jefa sun samar musu da maki 3.

A minti na 47 da fara wasa Aymeric Laporte ya jefa kwallo daya inda a minti na 97 Gabriel Jesus ya jefa kwallo ta 2.

A yanzu Manchester City na da maki 62 inda ta wuce Liverpool.

Everton na a mataki na 9 da maki 33.

Dan wasan Turkiyya Cem Tosun dake taka leda a Everton ya shiga wasan a minti na 80.Labarai masu alaka