Italian Cup: Atalanta ta yi wa Juventus wankin babban bargo

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta yi bankwana da gasar Italy Cup bayan da Atalanta ta yi mata wankin babban bargo da ci 3 da nema.

Italian Cup: Atalanta ta yi wa Juventus wankin babban bargo

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta yi bankwana da gasar Italy Cup bayan da Atalanta ta yi mata wankin babban bargo da ci 3 da nema.

'Yan wasan Atalanta Thimothy Castagne a minti na 37 da Duvan Zapata aminti na 39 da 86 ne suka jefa kwallaye a ragar Juventus. A yayin wasan mai horar da 'yan wasan Juventus Massimo Allegri ya samunjan kati saboda korafi kan alkalin wasan.

Haka zalika Kyaftin din Juventus Giorgio Ghiellini ya ji ciwo a minti na 25 da fara wasa wanda hakan ya sanya aka fitar da shi.Labarai masu alaka