Fiorentina ta doke Roma da ci 7 da 1

A wasan quater final na gasar zakaru ta Italiya kungiyar kwallon kafa ta Fiorentina ta doke Roma da ci 7 da 1.

Fiorentina ta doke Roma da ci 7 da 1

A wasan quater final na gasar zakaru ta Italiya kungiyar kwallon kafa ta Fiorentina ta doke Roma da ci 7 da 1.

A wasan na quater final dan wasan Fiorentina Federico Chieste ya jefa kwallaye uku.

Sauran 'yan wasan da suka jefa kwallo su ne: Luis Muriel, Marco Benassi da Giovanni Simeone (2).

Dan wasan Roma Aleksandar Kolarov ne ya jefa kwallo daya inda dan wasa Edin Dzeko ya samu jan kati a minti na 72.

Fiorentina za ta fafata a wasan kusa da na karshe da Atlanta ko Juventus da za su yi wasan quarter final a nan gaba.


Tag: Italiya , Gasa , Wasa

Labarai masu alaka