Infantino: Za a iya buga wasu wasannin FIFA 2022 a Kuwait

Shugaban Tarayyar Kwallon Kafa ta DUniya FIFA Gianni Infantino ya bayyana cewa, akwai yiwuwar a buga wasu wasanni a kasar Kuwait a yayin gasar Cin Kofin Duniya ta 2022 da za a yi a kasar Katar.

Infantino da ya ziyarci Kuwait don kallon wasan karshe na gasar Yarima Mai Jiran gado na Kuwait ya zanta da manema labarai inda cewa, za a iya buga wasu wasannin gasar ta FIFA 2022 a Kuwait din.

Infantino ya kara da cewa, ya yi wuri a kawo batun kara yawan kungiyoyi daga 36 zuwa 48 inda ya ce, matukar hakan ta tabbata to za a samu akrin mahalarta gasar daga nahiyar Asiya.

Shugaban na FIFA ya kuma fadi cewa, ya ji dadi da samun kungiyar kwallon kafa ta mata ta farko a Kuwait kuma ya kamata dukkan kasashe su yi koyi da Katar.Labarai masu alaka