Manchester ta fatattaki Arsenal

Manchester United ta doke Arsenal da ci 3 da 1 a zagaye na hudu na gasar cin kofin kalubale ta kasar Ingila wato FA Cup,abinda ya ba ta damar cimma matsayi na gaba.

Manchester ta fatattaki Arsenal

Manchester United ta doke Arsenal da ci 3 da 1 a zagaye na hudu na gasar cin kofin kalubale ta kasar Ingila wato FA Cup,abinda ya ba ta damar cimma matsayi na gaba.

Manyan kungiyoyon kwallon kafan biyu sun kara a filin wasa na Emirates da ke Landan,babban birnin kasar Ingila,inda Alexis Sanchez ya zura kwallo na farko a dakika ta 33,Jesse Lingard ya saka kwallo na biyu a minti na 33 sai kuma Anthony Martial wanda ya zura kwallo na uku a ragar Arsenal a minti na 82.

Maki daya tak na Arsenal ta same shi sakamakon wani kwallo da dan wasanta Pierre-Emerick Aubameyang ya zura a kwallon Manchester a dakika ta 43.

Kungiyar Manchester wacce tauruwarta ta fara haskawa tun bayan da dan asalin kasar Noway Ole Gunnar Solskjaer ya fara jan ragamarta,ta cimma nasari a dukannin wasannin 8 da 'yan wasanta suka buga,inda ta kuma riki matsayi na 5 a jerin kungiyoyin kwallon kafa wadanda suka taka rawar a zo a gani.

Dan wasan Arsenal dan asalin kasar Turkiyya,Mesut Özil ya shiga filin wasa a minti na 64 bayan ya kwashe lokacin mai tsawo ba tare ya saka taguwarsa ba,amma bai sa'ar taka wata muhimmiyar rawa a karwarsu da Manchester.Labarai masu alaka