An nemi jirgin saman dake dauke da Sala an rasa

Jirgin saman dake dauke da wasan kwallon kafar Ajantina Emiliano Sala ya bata inda ba a samu wani sakamako ba a binciken kwanaki 2 da ake gudanarwa.

An nemi jirgin saman dake dauke da Sala an rasa

Jirgin saman dake dauke da wasan kwallon kafar Ajantina Emiliano Sala ya bata inda ba a samu wani sakamako ba a binciken kwanaki 2 da ake gudanarwa.

‘Yan sandan Guersey sun fitar da sanarwar cewa, duk da tsaurara bincike a rana ta biyu wajen neman jirgin amma ba a samu wasu bayanai ba.

An bayyana sunan direban jirgin da ya bata da David Ibbotson kuma bayan wani taro da za a gudanar ne za a dauki matakin ko za a ci gaba da neman jirgin ko kuma za a dakata.

Jirgin saman ya tashi a ranar 21 ga Janairu daga garin Nantes na Farasa zuwa Cardif Babban Birnin Whales inda ya bace a saman tekun Mansh.

Emiliano Sala ya bar kungiyar Nantes ta Faransa zuwa Cardiff City a ranar 19 ga watan Janairu kan fan stalin miliyan 19.Labarai masu alaka