Real Madrid ta doke Sevilla FC

Kungiyar kallon kafa ta Real Madrid ta doke Sevilla FC da ci 2 da 0 a wasannin La Ligar kasar Spain.

Real Madrid ta doke Sevilla FC

Kungiyar kallon kafa ta Real Madrid ta doke Sevilla FC da ci 2 da 0 a wasannin La Ligar kasar Spain.

A karawarsu ta farko,kungiyoyin biyun wadanda suka shiga mako na ashirin (20) na La Ligar Spain da kafar dama, sun yin kunne doki.

A minti na 78 dan wasa Carlos Casemiro ya fara zuro kwallo na farko na Real,inda takwaransa Luka Modric kuma ya zuro kwallo na biyu a minti na tasa'in da biyu (90+2) a ragar kungiyar Sevilla FC.Abinda yasa Real ta lallasa Sevilla FC da ci 2 da 0.

Wannan nasarar ta bai wa Real Madrid damar tara maki 36 tare da kasancewa a matsayi na uku a  sahun kungiyoyin da suka taka rawar a zo a gani a gasar ta bana,inda Sevilla FC kuma, ke mara ma ta baya da maki 33 a matsayin ta hudu.Labarai masu alaka