Rana Irin ta Yau 20.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 20 ga watan Janairu.

Rana Irin ta Yau 20.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 20 ga watan Janairu.

Ranar 20 ga watan Janairun shekatar 1921 ne 'yan majalisar dokokin Turkiyya suka amince da kundin tsarin mulkin kasarsu na farko mai taken "Teşkilatı Esasiye".A washegarin yakin duniya na farko da kuma durkushewar Daular Musulunci ta Usamniyya,Turkawa sun gudanar da gaggarumar gwagwarmaya don kwato 'yancinsu da karfi da yaji ta hanyar kafa majalisar wakilansu ta farko a birnin Ankara a ranar 23 ga watan Afrilun shekarar 1920 a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Turkiyya,marigayi Mustafa Kemal Atatürk.Manufar wannan sabon kundin tsarin mulkin ita ce, karkata alkiblar Turkawa daga mulkin Usmaniyya wanda cibiyarsa ke a Santambul don komawa kacokal zuwa ga mulkin Jamhuriyya wacce al'uma ta kafa ba tare da an gindaya ma ta  "Sharadi ko da daya tilo ba".

Ranar 20 ga watan Janairun shekarar 1990 ne aka aikata laifin kisan gillar Yanvar a Baku,babban birnin kasar Azabaijan.Wannan kazamin kisan kiyashi ya biyo bayan tashe-tashen hankulan da suka barke tsakanin kabilun Turkawan Azeri da kuma al'umomin Kirista na Armeniyawa a ranar 13 ga watan Janairu,inda sojojin Tarayyar Soviet ta kusa kai Baku a tsakiyar daren 19 ga watan Janairu ya zuwa safiyar 20 ga watan Janairu tare da kashe kabilun Azeri babu sani babu sabu.Tankokin yaki na Rasha wadanda suka mamaye Baku sun yi sanadiyyar garkame akalla mutane 400.Burin Rashawa na karya gwiwa da kuma toshe bakin kabilun Azeri wadanda ke fafutukar cin gashin kai ta hanyar yi musu kisan gilla ya yi matukar fusata duniya wacce ta yi caa kan gwamantin Moscow.Daga bisan an ayyana 20 ga watan Janairu a matsayin "Ranar Shahidai" a kasar Azabaijan.

Ranar 20 ga watan Janairun shekarar 1996 ne a karo na farko aka gudanar da zabe a Falasdinu,inda marigayi Yaser Arafat ya zama shugaban kasa na farko na kasar.Falasdinu dai na kunshe da dukannin sassan Isra'ila, Zirin Gaza da kuma yankin yamma da gabar kogin Jordan.Tun farkon karni na 20 ya zuwa yau, kabilun Larabawa da na Yahudawa ke ci gaba fafata kazamin yakin da kawo yanzu ya ki ci ya ki cinyewa a wadannan yankunan wadanda mabiyan addinan Yahudanci,Kiristanci da na Musulunci suka yi imani cewa tsarkakku ne.Falasdinawa sun ayyana cin gashin kansu a ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar 1988 a Aljeriya a karkashin tutar kungiyar kwato 'yancin kan Falasdinu da Yaser Arafat ya kafa.Sama da kasashe dari wadanda a ciki har da Turkiyya ne suka amince da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa mai cin gashin kai.
 Labarai masu alaka