Kungiyar Kwallon Kafa ta Masu Kafa Daya ta Turkiyya ta zo na biyu a gasar kasa da kasa

Kungiyar Kwallon Kafa ta masu kafa daya ta Turkiyya ta zo na na biyu tare a lashe kambin azurfa a gasar kasa da kasa da aka gudanar a kasar Mekziko.

New folder (2)/amputee_3.jpg

Kungiyar Kwallon Kafa ta masu kafa daya ta Turkiyya ta zo na na biyu tare a lashe kambin azurfa a gasar kasa da kasa da aka gudanar a kasar Mekziko.

An buga wasan na karshe a garin San Juan de los Lagos na Mekziko inda danw asan Turkiyya Serkan Dereli, ya zubar da kwallo bayan pasin da Rahmi Ozcan ya ba shi A minti na 24 da fara wasan ma 'yan wasan Turkiyya Rahmi Ozcan da Shehmus Erdinc sun buga kwallo da ta daki turke ta dawo. Haka aka tashi wasa babu wanda ya jefa kwallo a raga tsaknin Angola da Turkiyya.

An kara lokaci na mintuna 10 sau 2 inda a nan ma dai kungiyoyin 2 ba su jefa kwallo a raga ba.

Sakamakon haka ya sanya dole aka yi bugun daga kai sai mai tsaron gida inda Turkiyya ta fitar da 'yan wasa da suka hada da: Barış Telli, Muhammet Yeğen, Fatih Şentürk da Rahmi Özcan da Osman Çakmak. 'Yan wasanta 4 sun jefa kwallayensu amma kyaftin Osman Cakmak ya zubar wanda hakan ya ba wa Angola nasara a kansu da ci 4 da 5.

Angola ta zo na farko Turkiyya kuma na biyu a gasar ta kasa da kasa ta wasan kwallon kafar masu kafa daya.

'Yan wasan na Turkiyya sun yi matukar bakin cikin gaza lashe gasar ta bana inda suka dinga zubar da hawaye.

A shekarun 2007, 2010, 2012 da 2014 'yan wasan Turkiyya ne suka lashe gasar amma a wannan karon sun zama na 2.Labarai masu alaka