Dan Najeriya dake taka leda a wata kungiyar kwallon kafar Turkiyya ya rasu

Dan Najeriya mai shekaru 23 mai suna Ekundayo Ebenezer Mawoyeka dake taka leda a kungiyar Saraykoyspor ta lardin Denizli na Turkiyya ya rasu a lokacinda ake tsaka da buga wasa.

Likitoci sun bayyana cewar dan wasan ya gamu da bugun zuciya wanda ya rasu a asibitin da aka kai shi.

Dan wasan ya yanke jiki ya fadi a mintuna na 35 da fara wasan da kungiyarsa take bugawa da Yesilkoyspor.Labarai masu alaka