Mutane da dama sun jikkata sakamakon turmutsutsu a Madagascar

Akalla mutum 1 ne ya rasa ransa yayinda wasu 40 suka jikkata sakamakon turmutsutsu da ya afku a a wajen shiga filin wasa a Madagascar.

Mutane da dama sun jikkata sakamakon turmutsutsu a Madagascar

Akalla mutum 1 ne ya rasa ransa yayinda wasu 40 suka jikkata sakamakon turmutsutsu da ya afku a a wajen shiga filin wasa a Madagascar.

Labaran da BBC ta fitar na cewa, an samu turmutsustu a kofar shiga filin wasa da ke Antananarivo Babban Birnin Madagascar inda jama'a suka je don kallon wasan da kasar za ta yi da Sanagal a wani bangare na wasannin share fagen halar gasar kasashen Afirka.

Dubunnan mutane masu sha'awar kwallon kafa ne suka yi turmutsutsun shiga filin wasan a lokaci guda ina mutum 1 ya mutu, wasu 40, wadanda biyu daga cikinsu ke cikin halin rai mutu kwakwai suka jikkata.

Ana yawan samun turmutsutsu a kasashen Afirka sakamakon rashin kula wa da jama'a yayin shiga filayen wasa.

A shekarar da ta gabata mutane 17 Angola, a Malawi 8 da suka hada da yara kanana 7 ne suka mutu sakamakon turmutsutsun da aka samu a filayen wasanni.Labarai masu alaka