FIFA ta sanar da wadanda za su fafata a gasar fitar da zakaru a bana

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta sanar da sunayen mutanen da za su fafata a matakin karshe na neman zakaran dan wasa, mai horar da 'yan wasa da ya fi kowanne, mai tsaron gida da wanda ya fi jefa kwallaye mafiya kyau.

'Yan wasa 3 da za su fafata a matsayin dan wasan da ya fi kowanne su ne, Modric daga Real Madrid, Ronaldo daga Juventus sai Salah daga Liverpool.

A masu neman mai horar da 'yan wasa da ya fi kowanne akwai tsohon kocin Real madrid Zinedine Zidane da ya lahe matsayin sau 3 a jere, Mai horar da 'yan wasan Faransa Didier Deschamps da mai horar da 'yan wasan Kuroshiya Zlatko Dalic.

A bangaren masu neman mai tsaron gida da ya fikowanne akwai na Faransa Hugo Lloris, Kasper Schmeichel na Leichester City da kuma Thibaut Courtois na Real Madrid.

A ranar 24 ga Satumba za a zabi zakaru daga cikin wadannan mutane dake takara.Labarai masu alaka