An kammala gasar tseren babura a kwazazzabai ta duniya da aka yi a Turkiyya

An kammala gasar tseren babura a kwazazzabai ta duniya a waje mai tsayi da fadin mita dubu 800,000 a garin Afyonkrahisar na Turkiyya.

2018/09/afyon_01.jpg
2018/09/moto_004.jpg

An kammala gasar tseren babura a kwazazzabai ta duniya a waje mai tsayi da fadin mita dubu 800,000 a garin Afyonkrahisar na Turkiyya.

An kammala gasar ta World Motorcross ta (MXGP) , MX2 da MXGP cikin nishadi.

An ba wa dukkan 'yan wasan da suka yi nasarar lashe kambi kyaututtuka bayan kammala gasar.

A bangaren MX2 Pauls Jonass dan aksar Lethonia na kungiyar Bull KTM ya zo na farko,dan kasar Denmark Thomas Kjer Olsen na kungiyar Rockstar Energy Husqvama ya zo na 2 sai dan kasar Amurka Thomas Covington na kungiyar Rockstar Energy Husqvarna da ya zo na 3.

A bangaren MXGP kuma dan kasar Holan na kungiyar Bull KTM Jeffery Herlings ya zo na daya, Tim Gajse dan kasar Sloveniya na kungiyar Team HRC ya zo na biyu sai dan kasar Beljiyom Clement Desalle daga kungiyar Monster Energy Kawasaki da ya zo na 3.

 Labarai masu alaka